Mas'udu Dan Masani Shinkafi |
_Ma'asumiya Nigeria News Updates_
*Tare da Wakilinmu Mas'udu Dan Masani Shinkafi*
Matsalar “Hacking” na Facebook account wata babbar matsala ce da ta dami kowa a wannan lokaci. Da yawa cikin mutane sun fada tarkon wadannan mugayen mutane (Hackers), inda zaku ga cikin mutane biyar, sai an samu biyu ko ukku da ko dai an taba Hacking na account dinsu, ko kuma account din wani nasu da suka sani. A cikin wannan kasida tamu ta yanzu, zamu yi muku bayani dalla-dalla akan yanda zaku iya kwato Facebook account dinku daga hannun Hackers bayan sun samu nasarar yi muku Hacking.
A cikin kasidarmu da ta gabata, mun yi sharhi sosai akan dalilan da suke sanyawa ake Hacking Facebook account na mutane tare da kuma hanyoyin da zaku bi wajen Kare kanku daga fadawa a hannun wadannan miyagun mutane .
A wannan kasida kuma, zamu zayyano muku matakan da zaku iya dauka idan na yi Hacking na Facebook account naku domin maido da shi.
Matakan da Ake bi wajen kwato Facebook Account Daga Hackers
1. Da farko zaku ziyarci wannan adireshi kamar haka: https://www.facebook.com/hacked
2. Sai ku taba inda aka sanya “My Account is Compromised”
3. Daga nan zaku shiga wani shafi inda za’a bukaci ku sanya Username (email) da kuma password dinku. A inda aka sanya
“Email Address or Phone number” , zaku sanya email dinku ko kuma lambar wayar da kuke amfani da ita (ko kuma ma sunanka da kake amfani da shi a Facebook din). Inda aka sanya Password kuma zaku sanya tsohon password din da kuke amfani da shi kafin a yi hacking din account din, sai ku taba inda aka sanya “Log In”.
4. Tabbas tunda kun sanya tsohon password dinku, za’a ce muku ne “Wrong Password” ko kuma “Incorrect Password”, kada ku damu. Sai ku taba inda aka sanya
“Forgotten Your Password” . Idan ka sanya email dinka ko kuma lambar waya, za’a nuno maka account dinka sai ka zaba.
5. Bayan ka zabi account dinka, zasu turo da wani code zuwa lambar wayarka ko kuma email dinka tare da bukatarka da ka sanya wannan code din da suka turo maka a wani dan wuri da zasu baka.
6. Bayan kun sanya code din sai ku taba “Verify”, wannan zaya kai ku zuwa wani page din inda za’a bukaci da ku sanya sabon password da kuke bukata.
7. Da zaran kun sanya sabon Password din sai kun sanya Login !
Wadannan sun hanyoyin da zaku iya bi idan anyi hacking na Facebook account dinku domin kwato shi daga wadanda suka yi muku wannan ta’asa da rashin mutunci!
Idan kuna da wata tambaya akan wani abu da baku gane ba, to zaku iya yin comment a nan kasa domin samun amsar tambayarku.
Tare da wakilinmu
______Mas'udu Dan masani Shinkafi 08149993999_______
Tags:
Yanar gizo