Nigeria |
🌎ma'asumiyya Nigerian news update
Daga wakilinmu Jibril Usman Sarki
A wannan zamani da kuma yarda muke ciki a yanzu, ta ko'ina zakaci karo da wasu irin yanayi wadanda suka hada da yanayi. stadar rayuwa ta fuskaci kayan masarufi, ruwansha, wutan lantarki, matsalar hanya, sata, yan iskangari , dakuma uwa uba shine zaluncinda mahukuntar kasannan 'Nageria' sukema talakawansu.
Sannan Irin wadannan mastaloli nima yau nastinci kaina a wani muhalli da mutane suke fama da mastaloli wadanda naga yadace ace indanyi magana akai, koba komai shuwagabannin wanan kasar Susan halinda talakawansu sukeci.
Dayake abubuwan sunada yawa nikeso inyi magana akai, Amman zanso inraba maganar gida hudu ne tayanda zanyi bayanin ko wanne, tayadda mai karatu zaiji saukin fahimtar sakon.
sune kamar haka
(1) Ruwa da wuta.
(2) Sara suka.
(3) Rigima tsakain matasa had kaji anacewa anrasa rai.
(4) kwace.
(5) stadar rayuwa.
A cikin wadannan mastaloli yanada wahala kara sasu ako ina afadin kasar nan ba, musamman abinda yashafi mastala ruwa da wuta! Wanda sanin kowane wannan gwamnatin takasa magance wadannan mastaloli. kuma kowani shugaba idan yazo yakin neman zabe yakanyi kamfe ne da wadanan abubauwa, Amman abintakaici har ynzu ankasa magance wanan matsalolin da suka addabi jama'ar kasar nan.
Har wala yau mutanen suna fama da wasu yan iskan matasa da suka dauka kisa ba'abakin komaiba suna sheke ayarsu ta yanda sukaga dama, hukuma kuma tayi shiru da bakinta. Wanda kuma hakan yana sanadiyar salwantar mutane da dama harta wadanda basujiba basuganiba, Wanda kuma yakamata adau mataki Don ganin anhana aika aika da yan iskan keyi a gari.
Sai kuma rigima stakanin matasan unguwa da kuma yan kato da gora (yan kwamiti? fa take nema taza wani Dan karamin yake sanadiyar, takurawa da wulakancin da yan kato da gora sukema ma matasa, har takai sukanbi mutu hargida idan sunganshi da gashi suyi masa aski da duka koda kuwa waye shi Wanda yayi sanadiyar suma matasa suka fara takon saka dasu, da musayan Sara da suka a tsakaninsu, kuma hakan yana haifarda mastala. Wanda naruwan shi ta shafeshi.
Saikuma yanzu stadar rayuwa da ake fama da ita ta ko ina har takai ga yanzu baza'a iya gane almajiri da Wanda ba almajiriba sabida kowa bara yake akan titi a gidaje da sauran wurare, zakasha mamaki da tausayi idan kaga yanda mata da yara suke biyar gidaje suna buga kofa sunacewa ataimaka musu da abinda zaauchi wlh yayansu na gida tunsafe ba abinda sukachi, Almajirai sukan sha wahala wajan neman abinda zasuci sabida gidajen da suke zuwa suma suna famada yanayi, kai da zanzauna ina karanta matsala ya isheka rubuta litafi.
Wanan a takaice kenan akan irin yanayi da mastaloli da mutane suke fama dashi a muhalinda nasamu kaina ina zama amastayin dalibi (student) ina fatan wanan yanayi da mastaloli yazo karshe da wuri, kuma ina kiraga gwannatin Nigeria akan tana tafiya tare da duba baya dan ganin halinda talakawanta sukeciki. Daga karshe ina addu'a Allah ya kara kawo mana zaman lafiya a stakanin mu baki daya
~sahannu~