* MA'ASUMIYA NIGERIAN NEWS UPDATES
Abinda mutane suka kasa ganewa kenan game da ma'anar bauta, a tunaninsu bauta ta taqaita ne kawai ga sujudah da abu.Amma a haqiqanin ma'ana, bauta tana nufin bin umarni ne da kuma hanuwa daga abinda aka haneka.
Ko da bautar Allah da ake magana, ai ba wai yin sallah, azumi, Hajji da bayar da zakkah bane bautar, a'a, umarnin da ya bayar ake bi shine bautar. Domin in da ace ba abi umarnin nasa ba da dukkan wadannan abubuwa ba ayi su ba.
Idan muka dunqule magana, bin abinda aka ce kayi da barin abinda aka ce ka bari shine bauta. In da za a wayi gari Allah yace yi ko kada kayi, sai kuma aka sami wanda ya sabawa fadin Allah, kai kuma ka bi ta wanin Allah, to, shi kake bautawa ba Allah ba.
Allah ya zargi Yahudu da Nasara yadda yake cewa,
" SUN RIQI AHBAR DA RUHBAN NASU (Malumansu) ABIN BAUTA KOMA BAYAN ALLAH ".
Sai wani da ake kira Adiyyi Bn Hateem yace, yaa Ma'aikin Allah, mu fa ba ma bauta musu. Sai Manzon Allah (S.A.W.W) yace," NA'AM, AI SU 'DIN SUNA HALATTA MUSU HARAM KUMA SUNA HARAMTA MUSU HALAL, SU KUMA SUNA BINSU (kan hakan), TO, AI WANNAN ITA CE BAUTAR TASU GARE SU ".
(Tuhfatul-Ahwaz na Tirmidhi, J:8, Sh:492).Yanzu ku ma irin wannan bautar kuke yiwa Buhari 'Dan Mai Agwagwa, domin Allah ya haramta zubar da jinane, shi kuma ya halatta.
Sannan kuma Allah ya halatta yin addinin muslimci da kuma bawa musulmai 'yancin yin addininsu, amma shi Buhari ya haramta. Ku kuma kuna biyayya gare shi kan hakan, tare da imanin duk abinda yake yi daidai ne. Kenan kuna nufin Allah shine ba akan daidai ba, kunga shi kuke bautawa.
TO, YAUSHE ZA KU DAWOWA BAUTAR ALLAH NE ???
Tare da wakilanmu na Bauchi Zone.
Tare da (Ado Isah Guda).
08137925034
Tags:
Tunatarwa