Da sunan Allah mai rahma mai jin kai"
Yan Uwa Masu bibiyar mu yau munzo muku da darasin mu na AHKAMUL ISLAM Wanda zamu ringa yinsa aduk mako dafatan zakuci gaba da kasan cewa damu Wanda ni Mudasir Bara'a Malunfashi. Zan ci gaba da kawo muku. A cikin wannan Shafi na MA'ASUMIYA NIGERIA NEES UPDATES
Da farko zamu fara da cewa;-
(1) Bai hallat ayi Taƙlidi da Asalin Addini ba abin nufi Mutum ya Karbi Zancen ba tare da wani dalili ba,
wajibi ne Akidar mutum a chikin asalin addini ta kasanche bisa dalili ne ko da a dunkule.
* Amma hukunche hukunche na Aiki afikhu Baligi na Zabi ya kasanche"
(A) mujtahidi:-sai ya kasan ce yana fito da hukunce hukunce *
(B) mukallodi:-wato yana karba hukunci daga mujtahhidi*
(C) muhtadi:-ya kasance yana da yakinin cewa aikinsa ya yi daidai da abin da ake bukata wato idan wasu mujtahidai suka ce wani abu ya haramta sannan wasu suka ce ya halasta to sai ya bar wannan aikinsa idan wadansu daga chikinsu(mujtahidai) suka CE an wajabta wannan Aiki"
kuma wasu suka ce mustahabbi ne zai yi aiki da shi saboda haka yabi umurnin hukuncin shari'a idan aka kaddara wannan aikin ya hau kan shi*
Baligi Wanda bai kasance mujtahidi ko muhtadi ba ya wajaba agare shi yayi taklid*"
**MUHADU AKARO NA BIYU DOMIN CI GABAN SHI
Tare da wannan Shafin mai Albarka
~Sa hannu~ Dan Masani
Amadadin Nura Isma'eel Baba
____HADAFINMU NEMAN YARDAR ALLAH____
Tags:
Ahkamul islam