🌎MA'ASUMIYA NIGERIAN NEWS UPDATE
daga wakilinmu...Muhammad magaji kastina
08167236663WANENE SAYYADI ALI (AS)?
Shidai Imam Ali qane ne a gurin Annabi s.
Abdullahi shine baban Annabi (sawa)
Abudalib shine baban Imam Ali (as)
Abdullah da Abudalib mahaifinsu daya wato Abdulmudallabi to kaga kenan nasabar Annabi daya ce data Ali shi Abdullah shine babba a cikin yayan Abdulmudallab sai Abudalib, Zubairu, Hamzata, Abbasu, Abulahabin, Haris, Algaidaku, Durarin, Alkanmu, sai kuma mata Safiyatu, Ummu Hakimin Albaidu, Atikatu, Urwa, Umaimatu, Barkatu daga cikin wa'annan 'ya'ya na Abdulmudallib Allah ta'alah ya azurta Abdullahi da kasancewa Baban Manzon tsira Annabi Muhammad (saww).
To haka kuma Allah cikin ikonsa ya azurta qanin Abdullah wato Abudalib, da kasancewa Baban mataimakin Annabi kuma wasiyin sa wato Aliyu bn Abudalib as sai shi Ali (as) ba Annabi bane amman yanada matsayi da girma a gurin Allah wanda Hadisai sun nuna girma da matsayi irin nasa wanda in ka cire Manzon tsira babu wanda ya kaisa a duk halittar Allah.
HAIHUWAR SA
An haifi Imam Ali (as) cikin watan Rajab sha ukku (13) ga wata, a cikin dakin Ka'abah wanda kafinsa ba haifi wani a ciki ba bayansa ma harya zuwa yau ba'a haifa ba.
Ya tashi a kalkashin kulawar Annabi (sawa) Tin yana dan shekara shidda da haihuwa Manzon Allah ya dauke shi zuwa gidansa lokacin yana tare da Nana Khadijat sun kuma cigaba da zama har zuwa wafatin sa
Matarsa ta farko itace Sayyidah Zahra yar Manzon Allah s. bai kuma auri wata ba har sai datai wafati ma'ana bai mata abiyar zama ba, sun haifi 'yaya biyar biyar amman na karshen su bai rayu a doran kasa ba sakamakon zubewar cikin sanadiyyar matseta da kyaure da wani fasiqi yayi gajerin sunayensu kamar haka.
(1) Hassan Al-mujtaba
(2)Husain Shaheed
(3)Zainabul Khubra
(4)Ummu kursum
(5)Muhsin
To bayan Wafatin Fatima Imam Ali ya sake auren wasu mata ga wasu gada cikinsu da haihuwar da sukayi a tare dashi.
(1)Khala bint Ja'afar Hanafi
haihuwar ta daya
(2)Ummu Habib
Haihuwa biyu
(3)Ummu Banin bint Hizan bint khalid
haihuwar ta hudu
(4)laila bint Mas'ud
haihuwar ta biyu
(5) Ummu Sa'id bnt Urwa ibn Mas'ud althaqafi
haihuwar ta biyu
Da dai sauran wa'anda bamu ambata ba.
FALALAR SA
To idan akai duba ga falalolin Ali bamasu qididdiguwa bane sai dai kawai mutum ya tabo ta wani janibin ya wuce ga qadan gada ciki.
yazo a Hadisi cewa wanda duk yaso yayi duba zuwa ga Adam a Iliminsa, zuwa Nuhu a tsoron Allah sa zuwa Ibrahim wajen Hakurinsa da kuma Musa wajen Kwarjinin sa da kuma Isah Wurin Ibadar sa to ya Kalli Ali Dan Abudalib.
Shine sarkin yaqin Manzon Allah (sawa) Ya halarci yaqoqin da Manzon tsira sune kamar haka
Badar
Uhud
khaibar
handar dss,
ya karya azzalumai masu yawa sai da ya kasance aduk inda aka ambaci Ali to Kafuri ko munafuki sai hantarsa ta kada.
Shine yazama mizani na gane kafuri da munafuki da kaga makiyin Ali to dayan cikin biyu kodai kafuri ko munafuki.
Matarsa itace shugabar Matan duniya!
Yaransu sune shuwagabannin Samarin gidan Aljanna to kuma duk wanda zai shiga aljanna saurayi ne!.
LABBAIKA YA MAULANA AMIRULMU'UMININ
Da duk itace alqaluma ne koguna kuma tawwada ne aljannu su zamo masu qididdigewa mutane masu rubutu to da basu rubuce Falalar ka ba ya Babul Ilmun Nabiy.
allahummasalli ala Muhammad wa'ali Muhammad
~sahannu~
Barrister Nuraddeen isma'eel
Tags:
Munasabobi