SHK Ibraheem Zakzaky
inji Sheik Zakzaky
Mai Nakaltowa, Sani Hamisu wakilin ma'asumiyya
Na'am idan ma muna da Al'umma, alal misali kana iya cewa Al'umma irin wadancen, kana nufin Kabilu? Sai mu ce, idan wani ma zai iya kumajin kabila, ya yi fada don kabila, sai mu ce masa, mu muna da abin da yafi kabilanci, ya fi bangaranci da 'yan kasanci! Wato muna da addini!
Addinin nan namu kuwa, ya hana zama dan kasa, ya hana kishi ko kumaji na' yan kasanci, ya hana kabilanci, ya hana bangaranci.
Manzon Allah (S) yana cewa "Wanda ya yi yaki domin kare kabilarsa (don kabilanci), ba shi a cikinmu " Wato ma'ana ba shi daga cikin jimlar musilmi.
Ba aikin musilmi ne ya yi yaki don kare kabila ba, yana yi ne don kare addini ne. Da aka tambaye shi, wani ya yi yaki domin jarumtaka, wani ya yi yaki domin ta'assubanci, wanne ne ya yi yaki 'Fisabiliah? Sai ya ce,"Wanda ya yi yaki domin kalmar Allah ta zama ita ce a sama shi ne (ya yi yaki) saboda Allah, shi ne Fisabilillah "Ana yin yaki ne saboda Allah (Fisabilillah). Saboda haka akan yi Shahada ne' Fisabilillah, amma ba a yi domin kabila, ba a yi domin kasa, ba a yi domin bangare.
Tana iya yiwuwa mutum ya ce min" ah to yanzu abin da kake cewa a takaice dai a koma ma addinin Musulunci ko? Sai na ce :eh haka ne. Abin da nake cewa Kenan, ba Ina wayo ba ne, haka ne ba wayo ba nake ba.
Yadda Bature ma bai mana wayo ba, ya ce ', Kafirci ya komar da mu, to Musulunci za mu koma! Dama shi ne jininmu, shi ne gadonmu, shi ne alfaharinmu, shi ne tarihinmu, shi ne mu! To ta yiwu wani ya ce, Ehen, za ka balle Arewa ne? Sai mu ce a' a, mu dai Musulunci muka ce maka za mu yi, kuma Musulunci ba ruwan shi da kudu ba ruwan shi da Arewa. Musulunci addini ne na Allah kuma kasa ta Allah ce.
~sahannu~
Barrister Nuraddeen isma'eel
Tags:
Jagoran Gaskiya