FILIN GIRKE-GIRKE
🌎MA'ASUMIYYA NIGERIAN NEWS UPDATE
Take da wakiliyarmu mejiddah Usman
Ayau mun kawomuku yanda akeyin shinkafar Karas da miyar naman shanu
Kayan hadi
Shinkafa
Karas
Nama
Tumatur
Attaruhu
Albasa
Tafarnuwa
mangyada
Magi
Yanda za ahada
Dafarko za a dora tukunya a Wuta harsai ruwan yatafasa sai adebo shinkafar daidai yanda akeso a zuba bayan tadan tafasa kamar sau uku sai a sauke da ruwan sanyi sai a zuba a mastami a ajiye agefe adauko Kara, asa a wanke sannan a yanka kanana a dora ruwan kadan bayan yatafasa sai a zuba wannan shinkafar da yankakken Karas.
arufe bayan mintuna kamar goma haka sai a sauke a dora tukunya bayan tayi zafi sai a zuba mangyada da yankakken albasa da tumaturi da tafarnuwa ayita juyawa har sai yasoyu' sannan a yanka naman shanu kanana asulala da gishiri da albasa bayan naman yayi laushi sai a zuba magi kori dai dai yanda akebukata sai azuba shinkafar a kwano da ganan sai cikawai yarage.
Kubiyo mu acikin sirin filin girke girke kashina biyu nan gaba insha Allah
~sahannu~
Barrister Nuraddeen isma'eel
Tags:
Filin Girke-Girke