Daga Shafin Ma'asumiya Nigeria news updates
Tare da Alkalamin Wakilinmu Sani Hamisu.
Sai batun kin yarda da Halifancin uku kafin Aliy (A.S) da kuma fifita Imam Aliy a kan sauran sahabai. Duk da cewa ban da nufin tsawaita magana cikin wannan mas'alar duk da muhimmancinta, saboda dan rubutun nan da ke hanunka ya yi kadan, watau bai isa ya dauki nauyin amsa tambayar nan yadda ya kamata ba. Illa Iyaka zan dan yi takaitaccen jawabi ne a kan mas'alar. Mai son karin bayani sai ya tuntubi ko ya samu Littafi na musamman insha Allah za ka samu amsar wannan tambayar, kila da ma wasu mas'alolin da suke da alaka da shi Imam Aliy (A.S) din.
Batun rashin yarda da Halifancin uku kafin sa kuwa, ba mu ce ba mu yarda da Halifancin bane haka kawai, a'a abin da muke cewa shi ne Imam Aliy (A.S) shi ne ya fi cancanta da Halifancin koma bayan waninsa. In ka so kana iya Fassara maganar duk yadda ka so.
Sai dai abin da nake son na hangar da mai karatu shi ne, Shi'a ba su yin addini cikin Jahilci da dimuwa a' a suna addininsu ne cikin ilimi da wayewa da amfani da hujjatul baliga.
Sa'annan batun kuma a ce Shi'a sune farkon kin yarda da Halifofi uku kafin Imam Aliy (A.S), sai in ce za ka iya fadin haka ta fuskaci biyu. Fuska ta farko ita ce jahiltar hakikanin tarihin Musulunci, tare da mugun takaituwar ka cikin bincike. Fuska ta biyu kuma ita ce, bin tsintar son rai da yarda da shiftar Iblis tsinanne!
Saboda ai inkarin Halifancin wasun Aliy (A.S) da suka yi kafinsa, aiki ne na wasu sahabban. Sune suka sunnata shi, kuma suka raya sunnar har zuwa yau dinmu wannan! Ka ko san cewa ba ka Isa ka hana mutane raya sunnar sahabbai ba don dukkansu adilai ne, kuma Kamar tashar taurari suke, duk wanda ka bi za ka shiriya!!
~Sa hannu~ DAN MASANI
Amadadin Editor Nura Isma'eel baba
Tags:
Taskar ilimi