'YAN SHI'A SUNYI MUZAHARA A BIRNIN ZARIYA CIKIN IZZA




🌎ma'asumiyya Nigerian news update

Daga wakilinmu Auwal Adam Sidi zaria

yan Shi'ar ne a cikin sahu

A yau Asabar 31-03-2018 yan uwa Almajiran Sayyeed Ibrahim Zakzaky hafizahullah na garin zaria da kewaye sun gudanar da gagarumar muzaharar murnan zagayowar haihuwan Imam Ali as, da muzaharar neman wannan gwamnati azzaluma da ta sako  jagoran harkan musulunci A 'Nigeria' Sheikh Ibrahim Zakzaky Wanda take tsare dashi har tsawon shekara biyu. da watanni bisa tsarewan zalunci
Duk da umarnin kotu tace asakeshi tare da biyansa diyya, Amma gwamnatin nageria tayi ko inkula bisa wannan al'amari.

Inda aka samu halartan daruruwan yan uwa  zaratan matasa manyansu da yaransu, Ana tafiya cikin tsari da raira wake masu dadi.
Andauko muzaharar ne daga bubban dodo cikin birnin zaria a inda aka rufe ita wannan muzaharar a kasuwar zaria, abudai sai Wanda kagani domin ansamu sabati.

Anyi muzaharar lafiya ankuma tashi lafiya,
Bayan Antashi kuwa ya watse! sai ga jami'an staro sunata barazana abisa kan titi amma dai basu kama kowa ba.


~sahannu~

Barrister Nuraddeen isma'eel

31/3/2018

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post