Daga Salis Umar mazan Zakzakiyya
-Marhaba bika ya habibi,-Dan uwa mai kyau na dubi,
-Farra'a zahiri da gaibi,
-Ka shigo ka zamo madubi,
--Munyi murna cike da hubbi da zuwa naka bada razanaba.
+
-Yan uwa sallama gareku,
-Ku fito ga dan uwanku,
-Nakune sashin jikinku,
-Mai bukatar ci gabanku,
--Saimu tashi mu massa barka marhaba bika dan uwa maraba.
+
-Dan uwa gamunan gabanka,
-Godiya mukayo gareka,
-Da kazo kaima mutaka,
-Rawar samuwar cigaba na harka,
--Rabbana ya dado hazaqa a gareka damu ilahi rabba.
+
-Wagga shafi dammu kayyi,
-Taimakon kaine da kayi,
-Don muzan mun sauke nauyi,
-Taimakon kanmu mukeyi,
--Lahira mu zamo a layin masu 'yanci bana firgitaba.
+
-Yan uwa ga kira garemu,
-Duk abunda ya dauru kanmu,
-Muyyi domin kalikinmu,
-Don shine mafita garemu,
--Zamu dace zamu samu rahamataka bada wahalaba.
+
-Dan uwa barister sannu,
-Gaisuwa ga nawa hannu,
-Jinjina baituka na zano,
-A gareka kawai na kunno,
--Kaina fara yiwa baiti bayan Sayyid da Ahalinsa babba.
+
-Addu'a ya rabbi Allah,
-Kai kayimu muketa sallah,
-Daukaka ko ina mu fillah,
-Ma'asumiyya aita tallah,
--Duniyar ko ina ta ratsa darajar zahra batulu babba.
+
-Kara kare malaminmu,
-Wanda yazzama hankalinmu,
-Ko ince gata garemu,
-Sidi Zakzaky mai gidanmu,
--Rushe 'ya'yayen asara masu cutarwa aba Nusaiba
Mawakin Salis Umar |
Tags:
Wakokin Harka