Ma'asumiyya Nigerian News Updates
Daga wakilinmu zaidu sulaiman shi'a
Ki kasan ce kamar wata kyakyawar fulawa ma abociyar kyau tare da daukar hankali tare da kyakkyawan kan shi ga mijin ki' Ki fuskan ce shi da mafi dadin kamshi da mafi kyawun tufafi, Manzon (saw) yace! Mumini bai amfana da komai ba bayan kiyaye dokokin ubangiji mafi alkhairi gare shi sama da mace ta gari' wanda idan ya kalle ta zata faranta masa rai.
Nana Aisha ta ce: mata ku kwadaitu da yin kwalliya ga mazajen ku, umamatu bintul Haris tana yiwa 'yar ta nasiha yayin auren ta tace!
Kar idon sa ya ga mummunan abu daga gare ki' Kar hanchin sa yaji kanshi daga gare ki sai mafi dadi.
Abdullahi bn Ja’afar yana yiwa yar sa nasiha yayin auren ta
Kwalliya ta zama dole a gare ki' ki sani kuma hakika mafi kyawun kwalliya shine da mafi kyawun turare shine ruwa (yana nufin kika sance mai yin wanka a koda yaushe, saboda idan babu wanka toh kwalliya da turare basu da amfani.
Wata mahaifiya tana fadawa yar ta a lokachin auren ta ce tana yiwa mijin ta kwalliya har sai data wuce shekara '70' a duniya, An tambayi wani mai hikima akan wacece kyakyawar mace Sai yace!
Itace wacce take samun damar isuwa ga idon mijin ta da hanchin sa da zuciyar sa.
Asma'u bn Kharija alfaza’riy ya aurar da yar sa Yayin da zai mika ta ga mijin ta, sai yace da ita! Ya ji kamshi atare dake haka zalika Kar yaga komai sai mai kyau daga gareki.
Yar uwa ta musulma Ko kina kwalliya domin mai gidan ki Shugaban ki Jagoran ki ? Ko kuma balligaza ce ki kazama a cikin gidan ki Ba kya yin kwalliya da ado sai zaki biki da unguwa ko kasuwa ko asibiti, Ya kamata mu gyara domin mu samu cikakken cigaba a cikin gidajen mu na aure.
Muhaɗu A kashi na biyu(2)
~Sahannu~
Barrister Nuraddeen isma'eel
Tags:
Taskar Ma'aurata