Masoyina
burinta kawai ta ganka sannan
idanuwana sun kasa ganin kowa
ba abin da suke son gani sai
kykyawar fuskarka abin alfaharina
Kaunarki ta mamayemini
Dukkannin sassan ilahirin jikina.
Tabi jini, tsoka, zuwa bargon
ashina. Domin zuciyata ita ce
ma’adanin surrikan tinaninka
a kodayaushe, Masoyina
Tabbas zuciya wata aba ce
waddda takan sa gangar jiki
rashin amfani idan ba ta samu
abin da take so ba ban san sonka
ya yi nisa haka a zuciyata ba sai da
Na zauna ina tunaninka kawai na ga hawaye
Na zuba daga cikin idona
hakika kaunarka ta kai mutukar kurewa a cikin raina.
Karkamanta dani ina jiran ka habibina Mas'udu Dan masani Shinkafi
Tags:
Kalaman Soyayya