Tabar Wasiyya Zuwa Ga Mawakin Nan Bayan Ciyon Ciki Yayi Sanadiyyar Wafatin Ta!!!

Muhammad Bala Afuwa


A tattaunawar sa da Wakilinmu na Ma'asumah Salisu umar..A cikin Shirin mu na <b>FILIN MAWAKAN HARKA</b> ku biyo mu domin jin Cikakkiyar Tattauawar.
.
Daga

Shafin MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATES

-

MA'ASUMIYA; Akramakkallah masu karatun mu zasu so ka gabatar musu da kanka musamman masu kaunar wakokin ka?

-
MUHAMMAD BALA AFUWA "Na'am, da farko Sunana Muhammad Bala Afuwa, kamar yadda aka sanni dashi, ni haifaffen garin Potiskum ne dake Jihar Yobe, sannan ni dalibin Makaranta ne, na kammala Karatun Diploma na a bangaran Health Administration anan Makarantar College of Administration and Business Studies dake nan Potiskum, a Shekarar 2015.
Yanzu ina sa ran fara karatun Jami'a Insha-Allah a wannan Shekarar, 2018.
Ina da Shekaru 24 a Duniya.
-

MA'ASUMYA- Wasu na ganinka matashi kuma ga tsagwaron baiwar Waka da Allah yayoma har wasu ke cewa gado kayi wasuma na musun haka to miye gaskiyar lamarin???

.
-
MUHAMMAD BALA AFUWA, "Gaskiyan Magana ban gaji Waka ba, Allah ta'ala ne cikin hikmarsa yamin wannan baiwan, Kuma Alhmdllh ina dada godemasa bisa wannan Ni'imar, kamar yadda naji wani Dan'uwa ke cemin bayan ya saurari wata Waka ta, mai Suna BUGUN ZUCIYA, yana mai cewa wannan bayin kaina bane, Allah ta'ala ne yai amfani dani wajan isarwa Al'umma sakon Zaluncin da akaiwa Sheikh Ibrahimul Zakzaky.
Da de makamantan su, na kanji sakonnin karfafa gwiwa harma daga AMAWA, wadda basu fahimci karantarwar Sayyed Zakzaky ba, kaga wannan na nuni da cewa sako na isa yadda yakamata, fatana da Addu'ata shine Allah ya tsarkake mana Zuciya muyi aiki da Iklasi.
Muh'd Bala Afuwa

MA'ASUMIYA- Kuna yawan wakoki Ku uku zuwa hudu har wasu ke ganin kamar wuyar wakace ke saku kuyi haka, wasu kuma ke ganin abotace da shakuwa tsakaninku miye gaskiyar wannan zancen??

-
MUHAMMAD BALA AFUWA, "Muna haduwa muyi Waka sama da Uku ma, hikman hakan shine WAHADA, kyautata alaka tsakanin bangarori Al'umman Musulmi,karkashin Jagorancin Sheikh Ibrahimul Zakzaky.
-

MA'ASUMIYA- kwanakkin baya munga ka wallafa wani rubutu na wata waka wadda Shk Muhammad turi yaji dadinta har yake cewa a dawo masa da ita baya wane dadi kaji da kasamu wannan batu na bayin Allah akanku??

-
MUHAMMAD BALA AFUWA, "Alhmdllh Masha-Allahu; bazan misalta dadin da naji ba, domin na samu sakonnin fatan Alheri da yawa daga wurin al'umma sanadin wannan wakan, kuma wani abun ban Sha'awa da ita akai amfani a Huseiniyyah kafin Mujaddadin wannan karnin ya fara jawabi, nayi Farin ciki sosai.
-

MA'ASUMIYA- Kayi wakoki da yawa amma yanzu wakokinka zasu kai Nawa kuma acikin su wace kafiso Sannan muna bukatar karero mana ita musamman baitukan da sukafi baka Sha'awa.?

-
MUHAMMAD BALA AFUWA, "Suna da yawa gaskiya, Lissafasu zai bamu aiki (Murmushi) , daya kace, amma biyu nafi so, SHUHADAN GIDAN ABBA da BUGUN ZUCIYA.
SHUHADAN GIDAN ABBA.
'Yau Shekara guda, da kashe mana Shuhada, wa Haidar Humeid wa Hammad Shuhadan gidan Abba'.
*Take nai tambaya ina su Humeid ina Haidaraa.
Sai akace dani sun tafi tuntuni sunyi kaura.
Zan muku tambaya ya Jama'a a garan ku luraaa.
In har babusu ya zan kalli Al-Zakzaky Abba?.
*Take na juya da baya tamkar zan kife don hawaye.
An kashe Muminai raunana Jikokin tagwaye.
Sai naga ga jini baibaye ko ina a kwaranye.
Sai naji Zuciya ta dada zafi wayyoni ya Rabba.
BUGUN ZUCIYA...
'Addini sai ansha Wahalaa sai mukara hakuri, Zakzaky Wakilin Qaem ne Labbaika Abu-Nusaiba '.
*Yauni aka sa a cikin kuraaa.
Makiya na watsamin 'kuraaa.
Tamkar ya Husein da gun Zahraaa.
Sun mini irin Ali Haidaraa.
Wadansu kafa wasu hannuna, sun jani akas bisa Titi, tufafina ya cude da jini basu so su barni da rai baaa....
-

MA'ASUMIYA, "Acikin wakokinka wace ce farko wacece tafi baka wahalar yi wace kuma tafi maka sauki ??

-
MUHAMMAD BALA AFUWA, "Wata Hip-hop Rap ce hakanan, duk cikarsu ba wacce taban Wahala, kama daga Wakan RIJAL (Hamasa), HIP-HOP freestyle, Wakan Juyayi, gaskiyan Magana ma ni kowace Waka cikin ikon Allah na iya, bana jin wahalar Waka, ba Launin da ban gwada naji na iya ba.
Lalle ina kara godema Allah bisa wannan baiwan da yamin, Allah ya taimakemu muyi amfani da ita ta fannin da ya dace.
-

MA'ASUNIYA -Akwai wata sister masoyiyar wakokin ka wacce ciyon ciki yayi sanadiyarta kamar yadda ka wallafa a shafin ka na sada zumunta bata hadu dakai ba hartabarwa kanwarta wasiyar hakan to wane Bakin ciki kaji a lokacin kuma wace hanya ka samawa masoyanka domin tozali dakai a saukake??

-
MUHAMMAD BALA AFUWA "Naji ba dadi da dukkan ma'anar ba dadi, ina rokon Allah ta'ala ya dada lullube ta da Rahmar sa. Gwagwarmaya muke, in bamu hadu a wannan Program din ba zamu hadu a wani, ga kuma Kafar sadarwa ta Zamani wato Social network, zamu iya magana kai tsaye da duk wadda ya bukaci hakan.
-

MA'ASUMIYA- Hmmm yanzu kana Iya kirkiro waka kayima shafin mu na ma'asumiya nan inda kake???

-
MUHAMMAD BALA AFUWA, "Insha-Allahul-Azeem
-

MA'ASUMIYA- To Ayi mana muji ko baiti biyuma?

MUHAMMAD BALA AFUWA, "Shafin Ma'asumiya, shafi mai Wallafa gaskiya, jama'a daku garzaya don kusan me akeyi a Duniya?...
*
Shafin Ma'asumiya wajibi ne ai muku jinjina.
Aikinku yana da Kyau Hazaka taku yau zan ayyana.
Daraja ta Imam Ali makiyanku a sasu su russuna.
Su ganoku acan sama Shafinku ya zagaye duniya.
-

MA'ASUMIYA, "Masha Allah, Allah ya saka

Wane kira ga reka ga matasanmu masu son shiga fannin waka kuma sunajin tsoro???

-
MUHAMMAD BALA AFUWA, "Na'am; kiran da zanyi ga Matasa 'Yan Uwa na masu Sha'awan shiga fannin Waka, kada su ji tsoron komai, in da rabon al'umma zasu amfana ta dalilin harshen su, kaga dalilin tsoronsa zai zama ya boyewa al'umma wani Karatu kenan, saide wani hanzari ba gudu ba, Naturally Waka baiwa ce, kuma Fuska ce, kowa da irin nasa, wani da ka ganshi kasan yafika kyau, to daure kayiwa kanka Kwalliya ta hanyar tsaftace harshe da dogon Nazari, wannan zai sa kafara hada kafada-da-kafada da Manyan Mawakan Duniya, koda baka kaisu kyan Waka ba, ta dalilin ma'ana za'a saurare ka.
-

MA'ASUMIYA- Wanne kira, Gargadi, ko shawara gareka a matsayinka na mawaqin Harka Islamiyya ga mawaqan da suke amfani da baiwarsu ta waqa wajen cin mutunci ko batanci ga wannan harka a idon duniya???

-
MUHAMMAD BALA AFUWA, "Su sani Allah ya basu aron lokaci ne yaga ya zasu tafiyar dashi, kuma hakika zai tambayesu akan wannan damar da yabasu ranar da Nadama bazata amfanar musu komai ba, su nutsu su kyale rudin Duniya, suyi abinda zai amfanar da kansu da Al'umman su, don Waka Sihiri ce, in ka kyautata aikinka ka kama Zuciyar mutane, inko akai akasin hakan ka fada tarko.
Fatanmu Allah ya tausaya mana.
Ya tsarkake mana Zuciya.
-

MA'ASUMIYA- Wane kira gareka ga yan uwanka mawaka a halin yanzu???

-
MUHAMMAD BALA AFUWA, "Su sani kowane aiki akwai kalubale cikin sa, musamman masu wakan Yabon Annabi da Ahlinsa, dole sai an daure.
Ba'a samun Aljanna cikin sauki, kuma munji Manzon Allah na cewa, duk wadda yamin baiti guda daya, yana da gidan bene a Aljanna.
Ita kuma Duniya gidan Jarrabawa ce, sai an daure sannan akaiga gaci.
-

MA'ASUMIYA- Menene Kiranka ga Gwamnati game da tsara Jagoranmu Sayyid Zakzaky (H)???

-
MUHAMMAD BALA AFUWA, "Ta sani cewa, kara mana wani Karatu take dalilin wannan Zaluncin da takeyiwa Jagoran Harkar Musulunci.
Kuma dole da dukkan ma'anar dole ta sake shi, tunda an tabbatar bashi da laifi, tabi Umarnin Kotu ta biyashi diyyar lalata masa wajan zama dataiyi, da kokarin bata masa suna bayan ta kashe dubban magoya bayansa.
-
MA'ASUMIYA- Minene fatanka na karshe anan gaba???

MUHAMMAD BALA AFUWA, "Allah tabbatar da Addinin Musulunci a Kasarnan, Alkur'ani yazamo abin hukunci a tsakanin Al'umma, da burin Shahada karkashin Sayyed Zakzaky.

-

MA'ASUMIYA- Muna godiya da lokacinka daka bamu.

MUHAMMAD BALA AFUWA. "Nima Nagode
Wakilin Ma'asumiya

Salisu Umar Mazan Zakzakyya

08021395846

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post