“Yanzu haka an yi mana qawanya. Tun sama da awowin 12 suke ta harbi !!!

Kasance da Shafin Ma'asumah Nigeria News updates, Shafi Dominic Kai da Al'ummar ka.



Tareda-__Mahadi Tukur Almizan.

To, bayan wannan jawabin da jagora, Shaikh Ibraheem Zakzaky(H) ya yi dangane da harim bam da masu kai hare-hare.

Bai samu amsa daga jami’an tsaro ko qaryatawa ba, sai kawai kawo harin da suka yi a ranar 12/12/2015 a Husainiyyah, inda daga nan suka wuce Gyallesu da Darur-Rahma da sauran wurare, suka kashe fiye da mutum 1,000, tare da jikkata da dama, suka qona wasu da ransu, suka kwashe gawarwaki suka je suka bizne su a ramukan bai-daya a qauyen Mando da ke gefen garin Kaduna.

Sun kwana biyu suna ruwan wuta a gidan Shaikh Zakzaky(H), sai da suka tabbatar sun kashe kowa, suka saka ma gidan wuta, sannan suka shiga suna neman Shaikh Zakzaky (H).

Sai a ranar Litinin 14/12/2015 suka gane inda yake, sannan suka bude wuta a zakin, suka kashe ‘ya’yansa guda uku a gabansa, da wasu almajiransa da ke tare da shi, sannan suka harbi matarsa da shi, suka ja su cikin jini suka tafi da su, yau fiye da shekaru uku suna tsare da su ba tare da wani dalili ba.

______ABIN DA YA FARU A WAQI’AR ZARIYA______
A yayin da waqi’ar Zariya ke faruwa, Sojoji sun shelantawa duniya cewa tare musu hanya ne aka yi, shi ya sa suka yi wannan bude wuta da kisa na ta’addanci. A daidai lokacin, sai kafar yada labarai ta BBC suka kira Jagoran Harka Islamiyyah Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), inda suka tambaye game da abin da ke faruwa, da kuma halin da ake ciki.

Haka ma wani mai suna Husaini daga Iran, ya kira Shaikh Zakzaky a waya da asubahin ranar Lahadi 13/12/2015 inda shi ma ya fada masa halin da ake ciki.

Ga abin da Shaikh Zakzaky (H) ya sanar da kafafen guda biyu a yayin da muka tattare su a waje guda:
“In mutum ya duba ‘site’ dinmu, musamman
www.harkarmusulunci.org na Hausa, zai ga an rubuta cewa ranar Asabar (12/12/2015) za a yi canjin tuta.
Tun ranar Litinin (7/12/2015) aka ba da wannan sanarwar.

Saboda haka zaunannen biki ne da ma. To sai ya zama kuma har wala yau su kuma sojoji suna ‘Passing out.’ To kuma sun saba in suna ‘Passing out’ sukan yi ‘Ceiling’ hanyoyi. Mu da yake za mu yi namu qarfe 5:00 na yamma, muna fata bayan sun tashi ne mu za mu tafi gun taron namu da za mu yi tsakanin qarfe 5:00 zuwa 6:00 na yamma.
“To, amma sai muka ji labarin an kai sojoji Husainiyya, sun yi ‘Taking Position.’ To, ba mu san dalili ba. Ana nan sai suna harbi a iska, daga nan kuma sai suka fara harbin mutane.”

“Dangane da batun cewa mun kai wa sojoji hari, har ma mun yi qoqarin halaka Tukur Buratai, to wallahi qarya ne! Ka san dai yau shekararmu 37 cur muna harkar nan; sau nawa muka taba kai wa wani hari? Soja yake ko dan sanda ko wani mutum.
Sau nawa soja na wucewa ta Husainiyya? Yaushe aka taba kai wa wani hari? Ina ganin da ma kame-kame suke yi.

“Da farko sun ce za mu yi taro ne mu kai ramuwar gayya don an kashe mana wasu mutane jiya a wani qauye da ake ce wa Gabari, kusa da Zariya. Daga baya muka ji cewa an yada wa sojojin jita-jitar wai mun kashe sojoji guda biyu. Sannan kuma qarshe, sai muka ji sun ce wai shi Janar Buratai ya tsallake rijiya da baya. To, ka ga wannan duk kame-kame ne, kamar da ma suna da shirin su yi wani abu ne, yanzu suna neman dalilin da za su ce sun yi wannan abin ne saboda shi.“Inda da gaske ne hari ne ake neman a kai, yaya za a yi a ce mu ne kawai aka harba, aka kashe, kuma ba ko daya soja da ya samu qwarzane? Su suke da bindiga, mu hannu sake mutane suka je, sanya tuta za su yi, ba fada suke yi ba.”

“Yanzu haka an yi mana qawanya. Tun sama da awowin 12 suke ta harbi a kan gidana. Sun rusa mana Husainiyya da manyan bama-bamai, yanzu kuma suna kawo hari gidana.

A yanzu haka ma suna harbin bangwayen gidan ne. Sun zo nan tun misalin qarfe 10:00 na dare ranar Asabar, kuma tun sannan harbi suke yi kawo lokacin da muke maganar nan.

Haqiqa rayuwata tana cikin hatsari. Amma ba abin da na iya yi. Allah ne kawai zai kuvutar da ni, saboda ba wata mafita. Sun riga sun yi wa gidan qawanya. Suna kowane lungu da zai iya kawo wa zuwa gidan nan.

“Ya zuwa yanzu da nake magana ba mu san adadin mutum nawa suka kashe ba. Amma dai a nan gidana sun kashe mutum 14.

Amma a Husainiyya sun kashe kowa da kowa da ke ciki, amma ba mu san adadinsu ba. Sun ma kama wasu da ransu, su kusan talatin, amma sun harbe su. Ya zuwa yanzu dai da muke magana wadanda suka kashe sun haura hamsin, kuma ci gaba da
harbi kawai suke yi.“Abin da za mu ce shi ne, mutane su kwantar da hankali. A halin da ake ciki yanzu akwai mutane a Husainiyya, kuma lallai soja sun kewaye wurin, don mun so mu je mu sa tutarmu mu watse, amma sun tsare hanyoyi ta ko’ina, sun hana a je wajen. Sun yi kwanton bauna a ko’ina a eriyan; ba mu san me suke nufi ba. Amma wannan al’amari dai bangare guda ne ke kidansa da rawarsa; shi ne bangarensu ba mu ba ne. Mu ana auka mana ne, ba mu ne muke fada da kowa ba, wasu ne ke fada da mu.
___________________________
Ma'asuma Nigerian News Update.
Visit maasumah.com.ng
Wakilinmu;
™_____Mahadi Tukur Almizan.
[Daga Littafin Yunkurin kashe Sheikh Zakzaky ashekaru goma ]

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post