Adinin Allah da ya aiko wa da Manzan ninsa. Ya aiko yan aiken sa ne ga dukkan mutane, domin suyi kira zuwa kalma guda shine: 'A bauta wa Allah shi kadai'.
Mun yarda cewa munyi imani da Allah da Manzon sa (S) sai kuma yazam a lokaci guda bama koyi da wannan shi Manzo din.
Hakan na nuna cewa; Bama aikata abinda muke tutiyar mun ginu akai, yakamata muzam kasu koyi da halaye na manzon Allah (S) mu dauki kawukan mu matsayin abu guda tushe guda, masu neman cimma manufa guda.
Dukkan mu yayan Adamu (As) ne, abin mamaki qabilanci, da yan kazanci ya hana mana bin gaskiya, mun dauki son ranmu mun muhimmantar dashi fiye da komi.
A kalla kamar yadda muke Musulmai muzam abin koyi ga dukkan kowa, kamar yadda Manzon Allah (S) ya zam madubi ga kowa, yai nasara da kyawawan dabi'un sa wajen kira zuwa ga hanyar Allah (T).
Da zamuyi amfani da wannan maganar ta Imam Ali Zainul Abideen (As) da zamu rage wasu daga cikin abubuwan dake raba kawukan mu da tunanin wani zai iya cutata mana.
Karanta kaji me Imam (As) Yace.....
A cikin zantukan sa na hikima yake cewa; "Me kake tunanin zai zo gareka na cutuwa idan ka dauki dukkan musulmi matsayin yan uwanka, makusantanka?
Ka dauki wadanda suka girme ka a matsayin iyayenka, kananu matsayin 'ya'yanka su kuma wadanda kuke kankankan a matsayin yan uwanka. Idan kayi haka wa kake tunanin zai cutatar dakai?"
Imam yaci gaba da fadi cedwa; "Duk lokacin da tunani ya zaiyarci zuciyarka ka fara raya kafi wani to, ka fara nazari kan wadannan abubuwan....
Idan mutum ya girmeka, to ka tunasar da kanka cewa; wannan fa ya fika a harkar addinin Musulunci domin yayi ayyukan alkairi (Kyawawan aiki) da yawa kafin kai.
Idan mutun ya kasance kafi shi skekaru to, ka tunasar da kanka cewa ya fika. Domin bai aikata ayyukan zunubi kamar yadda kai ka aikata ba.
Idan kuma mutumin kana tunanin kuna kankankan ne a shekaru to kayi tunanin ya fika, domin ayyukan sabon da ka aikata ka sani baka san nasa ba."
Imam (As) yaci gaba da cewa; "Kada ka taba daukar wani matsayin makiyinka, a maimakon haka ka dauke shi matsayin mara cutarwa kuma kada kaki karbar abotar sa koda ko kana tunanin bazai amfanar dakai ba."
Allahumma salli ala Muhammad wa Ali Muhammad.
Bin Haroun Sigau
08065008703
Tags:
Muhimman zantuka