Daga cikin sunayen Allah (T) akwai Mai rahma (ARRAHMAN), wato mai tausayi, mai kyautatawa, mai yin baiwa ga kowa da komai.
Wannan rahma tasa takan shafi komai da kowa, shi yasa yake azurta mai saba masa da ma mai yi masa biyayya, hatta ga dabbobi za kaga komai my muguntarta Allah na sauqaqa maka hanyar neman abincinta. Mu kuma yace mana mu kyautata musu (dabbobin) ta hanyar kisa ne ko kuma mu'amala.
Saboda wannan rahma ta Allah yasa mutane ke yin abinda suka ga dama, su nemi mulki da dukiya ta hanyar saba masa (Allah), alhali sun san yayi hani game da hakan.
Mutum zai iya kashe dan'uwansa don ya sami duniya, yayi tsafi don ya sami mulki, kuma yaci kudin ruwa (Riba) don ya tara dukiya.
To, wanda ya sami duniya ta hanyar irin wannan hanya za kaga yana farin ciki, wasu kuma kaga suna sha'awarsa.
Manzon Allah (S.A.W.W) na cewa;
" IDAN KAGA ALLAH YA BAIWA BAWA ABINDA YAKE SO DAGA DUNIYA TA HANYAR SABA MASA, TO, WANNAN ISTIDRAJI (shigo-shigo) NE (yake masa) ."
Sa'an nan ya karanto wannan ayar:
" YAYIN DA SUKA MANTA DA ABINDA AKA TUNATAR DASU SHI, SAI MUKA BUDE A KANSU QOFOFIN DUKKAN KOMAI (na mulki da dukiya), HAR A LOKACIN DA SU KAYI FARIN CIKI DA ABINDA AKA BA SU (na duniya) , MUKA KAMA SU KWATSAM, SAI GA SU SUNYI TSURU-TSURU (da idanuwansa) ."
(AN'AM, AYA TA 44)
- Musnad Ahmad, J:4, Sh:145
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034-08126385470
Tags:
Tunatarwa