Shi ne Abun koyi ga dukkan Muminai...
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED
Sai ma na rasa abin cewa a duk lokacin da na ji wasu masu kiran kansu da sunan maluntaka na cewa;
" BAI KAMATA ANA YIWA SHUGABA MUMMUNIYAR ADDU'AH BA DUK MUNIN HALINSA, DOMIN HAKAN SAI YA QARA MASA LALACEWA, KAMATA YA YI A RIQA YI MUSU ADDU'AR ALKHAIRI."
Amma ina tuna sunnar da Annabi (S.A.W W) ya koyar damu a aikace sai nayi musu uzuri da cewa, jahilci ne ko kuma kwadayi ke sa su yin wannan furuci da babu shi cikin koyarwar muslimci. Bisa yadda Annabi (S.A.W.W) ya koyar damu a aikace shine, shi dai azzalumin shugaba addu'ar halaka ake masa, amma raunana mabiya kuma sai ayi musu fatan shiriya.
Ga dai hujjata cikin Sahihul-Bukhari littafin da wadannan jahilai makwadanta suka yi imani da dukkan ingancin abinda yazo cikinsa, alhali wasu hadisan cikinsa qarya ne da qoqarin boye gaskiya.
KARANTA WANNAN:-Kuzo kuga Magajin Annabawa..
Bukhari yace, Abdaanu Bn Usman ya bamu labari yace, babana ya bani labari Shu'ubatu, daga baban Ishaq, daga Amruu Bn Maimun, daga Abdullahi (R.A) yace;Wata rana Manzon Allah (S.A.W.W) yayi sujadah, a kewaye da shi kuma akwai mutane mushirukai daga Quraishawa, sai ga Utbatu Bn Abiy Mu'aidin ya zo da dubin tsohuwar Raquma ya dora ta akan bayan Annabi (S.A.W.W), bai iya dago kansa ba har sai da Fadimatu (A.S) ta zo ta dauke shi daga bayansa (S.A.W.W), sai yayi addu'ah kan wadanda suka aikata haka.
Annabi (S.A.W.W) yace;
" YAA UBANGIJI KA ISAR MIN WANNAN CUTARWA DAGA QURAISHAWA.
YAA UBANGIJI KA ISAR MIN AKAN ABU JAHAL BN HISHAAM, DA UTBATA BN RABEE'A, DA SHAIBATA BN RABEE'A, DA UTBATA BN ABIY MU'AIDIN, DA UMAYYATA BN KHALAFIN, KO UBAIYI BN KHALAFIN!"
(Abdullahi yace), haqiqa na ga an kashe su kaf a ranar Badr, aka jefa su cikin Rigiya, sai da Umayyata, ko kuma Ubaiyi, domin shi mutum ne mai qiba (very fat), yayin da aka ja shi (a qasa) sai tsatsonsa ya tsittsinke tun kafin a jefa shi cikin Rijiya."
(Bukhari, hadisi na 3185).
Saboda haka sunnah ce yiwa azzalumi addu'ar halaka !
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08137925034
~ 21st November, 2019.
Tags:
Tunatarwa